1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: An karya doka kan 'yan gudun hijira

Ahmed Salisu
April 2, 2020

Kotun koli ta Kungiyar EU ta ce kasashen Poland da Hungary da Jamhuriyar Czech sun karya dokokin kungiyar bayan da suka ki amincewa su karbi kason da aka basu na 'yan gudun hijira domin su tsugunar da su a kasashensu.

https://p.dw.com/p/3aL0E
Europäischer Gerichtshof in Luxemburg
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Kotun koli ta Kungiyar EU ta ce kasashen Poland da Hungary da Jamhuriyar Czech sun karya dokokin kungiyar bayan da suka ki amincewa su karbi kason da aka basu na 'yan gudun hijira domin su tsugunar da su a kasashensu.

Kotun da ke da mazauninta a kasar Luxembuourg ta ce kin amincewa da karbar 'yan gudun hijirar da kasashen suka yi daidai ya ke da sanya kafa su yi fatali da irin shirin da aka yi don saukakawa kasar Girka wadda take ta fadi-tashi wajen ganin an rage mata nauyin da ke kanta na 'yan gudun hijirar da ke kasarta wanda wasunsu suka shiga tun cikin shekarar 2015.

Har wa yau matakin kasashen inji kotun karan tsaye ne babba ga irin dokokin da Kungiyar EU ta gindaya wanda ya kyautu a ce sun bisu sau da kafa. Ya zuwa yanzu dai kotun ba ta bayyana irin hukuncin da wadannan kasashen za su fuskanta ba.