Erdogan:"Turai na girban abin da ta shuka"
September 6, 2022A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Ankara, Erdogan na Turkiyya ya ce "Turai na girban abin da ta shuka, inda ya kara da cewa "Putin na amfani da duk wata hanya ciki har da iskar gas wajen rama wa kura aniyarta." Tun a jiya Litinin(05.09.2022) ne fadar mulkin ta Kremlin ta dakatar da amfani da jigilar iskar gas daga Rasha zuwa Jamus, saboda a cewarta takunkumin da kasashen Turai suka kakaba mata ya hana kula da bubutun Nord Stream yadda ya kamata.
Ita dai Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya takunkumi a kan man fetur da kwal da Rasha ke hakowa, amma takunkumin bai shafi iskar gasa ba. Yayin da a nata bangaren Turkiyya ke kyautata alakarta da Moscow da Kyiiv duk da kin mutunta takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha. Maimakon haka ma, Ankara na sayan wani kaso na makamashin daga Rasha a farashi mai rahusa