1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na shirin yin tonon silili

Gazali Abdou Tasawa
October 21, 2018

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin bayyana hakikanin gaskiyar abin da ya wakana a game da batun kisan dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/36ujI
Türkei Recep Tayyip Erdogan, Präsident
Hoto: Reuters/B. Szabo

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashi ne a gaban dubunnan jama'a a wurin wani kasaitaccen taron gangami da aka gudanar a wannan Lahadi a birnin Istanbul inda ya yi karin bayani yana mai cewa su masu neman shari'a ta yi halinta ne, kuma suna da cikakkun bayanai kan abin day a faru, kuma za mu bayyana wa duniya su a babban taron da jam'iyyarsa za ta gudanar a ranar Talata mai zuwa.

Mahukuntan Turkiyyar dai sun alakanta mutuwar dan jaridar da zuwan tawagar wasu 'yan kasar ta Saudiyya su 15 da suka je a birnin Istanbul a cikin wasu jiragen sama guda biyu a ranar biyu ga watan nan na Oktoba. 

A jiya Asabar ne dai a karon farko mahukuntan Saudiyyar a hakumance suka amince da mutuwar dan jaridar tare ma da sanar da daukar matakin korar wasu manyan jami'an gwamnatin biyar da kama wasu 'yan kasar ta Saudiyya su 18 a karkashin wani aikin bincike da Saudiyyar ta kaddamar kan wannan lamari. Sai a wannan lahadi sun bayyana cewa ba su da masaniya a game da inda gawar dan jaridar take ya zuwa yanzu.