1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya dorawa Turai alhakin Venezuela

Abdoulaye Mamane Amadou
February 5, 2019

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya, ya zargi Tarayyar Turai da neman hambarar da shugaban vénézuéla Nicolas Maduro da aka zaba a tafarkin dimukradiyya.

https://p.dw.com/p/3ClIF
Türkei Präsident Recep Tayyip Erdogan in Ankara
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/V. Furuncu

A yayin wani jawabinsa a kafar yada labaran kasar Turkiyya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya zargi kasashen na Turai, ya ce yanzu sun fahimci inda kungiyar Tarayyar Turai ta sanya gaba, musamman fakewa da suke yi da batun zabe daga bisani kuwa ta tayar da fitinar da ke iya kaiwa ga hambarar da mulkin Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela.

Shugaban na caccakar kungiyar ta Tarayyar Turan ne a daidai lokacin da wasu kasashe 19 na Turai suka amince da madugun hamayya na kasar Venezuela Juan Guaido a matsayin shugaba na riko.   

Erdogan da Maduro sun dade suna dasawa, wanda ko ranar 23 ga watan jiya jim kadan bayan soma boren kasar Venezuela, Shuga Recep Tayyip Erdogan ya kira Maduro, inda ya bukaci da ya ci gaba da rike matsayinsa na shugaban kasa.