1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Erdogan zai kawo ziyara Jamus

Zulaiha Abubakar
September 27, 2018

Shugaban kasar Turkiyya ya ja hankalin masu kyamar baki da ayyukan ta'addanci a Jamus da su rungumi akidar zaman lafiya yayin da yake shirin kawo wata ziyarar kwanaki uku da niyyar inganta alakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/35YYN
Merkel und Erdogan PK in Berlin 04.02.2014
Hoto: Getty Images

Shugaba Erdogan ya kara da cewar yana kyakkyawan zaton gwamnatin Jamus za ta yi duba cikin batun kungiyar malamin addinin Islaman nan Fethullah Gülen wanda kasar Turkiyya ke zargi da hannu cikin yunkurin hambarar da gwamnatin a shekara ta 2016 da kuma ayyukan ta'addanci.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta jima da tsami, sai dai takunkumin da Amirka ta kakaba wa Turkiyya ya tilastawa shugaba Erdogan neman hadin kan Jamus da kuma Kungiyar Tarayyar Turai don farfado da tattalin azikin kasar.

Jama'a sun fara gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da wannan ziyara ta Erdogan a wasu daga cikin manyan biranen Jamus .