1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G7: Jaddada goyon baya ga gwamnatin Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar AMA(Lateefa)
June 28, 2022

Shugabannin kungiyar kasashe masau arziki na G7 sun kammala taronsu a Jamus, inda suka aike da sakon hadin kai bisa la'akari da halin da ake ciki na rikicin mamayen Ukraine da Rasha

https://p.dw.com/p/4DNeZ
Taron G7 l Elmau 2022 | Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Taron G7 l Elmau 2022 | Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz Hoto: dpa

Shugabanin kasashen Birtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan kana da Amurka, sun cimma matsayar bada goyon bayansu ga Ukraine da kokarin da suke yi na ganin an rage dogaro da makamashin Rasha, da kara matakan hukunta Moscow.

Shugaban gwamnatin Jamus kuma mai karbar bakuncin taron na yini uku da ya gudana tsibirin Elmau da ke Bavaria Olaf Schol ya ce, kungiyar kasashen bakwai masu arziki na duniya za su ci gaba da kasancewa a bangaren Ukraine. 

Karin Bayani: Kasashen G7 na kara matsin lamba ga Rasha

"Za mu ci gaba da daukar nauyin wannan ya ki a siyasance da fannin tattali a wani mataki na gasawa gwamnatin shugaba Vladimir Putin tsakuwa a hannu. Dangane da haka, hadin kanmu yana da muhimmanci don cimma wannan buri. Kazalika zamu kalubalanci farfagandan Rasha na cewar, wannan rikici ne da kasashen yammacin Turai ke sukar hare-haren, duk da cewar duniya na kallon abunda Rashan ke aikatawa a zahiri da cewa ba haka lamarin yake ba".  

Taron G7 a Elmau | Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Joko Widodo
Taron G7 a Elmau | Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Joko WidodoHoto: Laily Rachev/Biro Pers Sekretariat Presiden Indonesia

Shi ma shugaba Emmanuel Macron na Faransa cewa ya yi babu yaddaRasha za ta ci galaba a wannan yakin da a cewarsa zai zo karshe nan da karshen shekara, inda ya bayyana harin makamai masu linzami na ranar Litinin a tsakiyar birnin Kiev da kasancewa "laifin yaki", harin da shi ma shugaban gwamnatin Jamus Scholz ya yiwa mummunar suka.

Karin Bayani: Martabar Scholz ta dawo a idanun Ukraine

"Harin makaman rokoki na jiya a tsakiyar rukunin shagunan sayayya na Kremenchuk kusa da birnin Kiev da  ya bar mutane da yawa mace da kuma raunata wadansu, ya kara tabbatar da cewar Putin na ci gaba da aikata zalunci a kan al'umma".

Fraministan Italiya Mario Draghi ya ce kasashen na G7 sun damu matuka kan yadda sojojin Rasha ke ke kara matsowa zuwa yankin gabashin Ukraine, sai dai shugaba Volodymyr Zelenskyy na da yakinin cewar, Uukraine za ta cimma nasarar yin martani.