1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Elfriede Jellinek 'yar kasar Austriya ce ta samu lambar yabo ta Nobel dangane da marubuta adabi

October 7, 2004

Kwamitin lambar yabo ta Nobel ya zabi 'yar kasar Austriya Elfriede Jellinek domin mika mata lambar yabo dangane da rawar da take takawa a rubuce-rubucen adabi da wasannin kwaikwayo

https://p.dw.com/p/Bvfq
Elfriede Jellinek
Elfriede JellinekHoto: dpa

Daruruwan ‚yan jarida ne suka yi cincirindo a kofar tsofon zauren cinikin hannayen jari na birnin Stolkholm, kamar dai yadda aka saba a kowace shekara, suna masu dokata domin jin sunan wanda ya za a mika wa lambar yabo ta Nobel dangane da bajinta a rubuce-rubucenm adabi a wannan shekarar. A cikin sanarwar da ya bayar babban sakataren kwamitin lambar yabon ta Nobel Horace Engdhal cewa yayi:

Lambar yabo ta Nobel akan bajintar rubuce-rubucen adabi dangane da shekara ta 2004 za a mika ta ne ga marubuciyar kasar Austriya Elfriede Jellinek dangane da rawar da take takawa a rubuce-rubucenta na hikayoyi da wasannin kwaikwayo, inda take amfani da wasu lafuzza masu fayyace banbance-banbancen dake akwai a tsakanin jama’a a harkokin rayuwa ta yau da kullum.

A wannan karon ma kwamitin ya cimma nasara wajen boye sunan mai nasarar samun lambar ta yabo har sai yau da rana. Mutane sun sha fama da rade-radi a game da mai rabon samun lambar ta bana ko Doris Lessing ce ko Joyce Carol Oates ko kuwa Isabel Allende. Ba wanda yayi tunani a game da Elfriede Jellinek dake da shekaru 58 da haifuwa, wacce kuma ta fara rubuce-rubucen adabi da wake tun tana ‚yar shekaru 21. A cikin rubuce-rubucenta bata shayin tsage gaskiya wajen bayyana matsaloli na rayuwa ta yau da kullum da yadda ake danne hakkin mata da kuma son kai na dan-Adam. Jami’ar ta rubuta litattafan adabi da hikayoyi da kuma wasannin kwaikwayo masu tarin yawa, wadanda wasu daga cikinsu ake nunarwa a gidajen wasannin kwaikwayo na kasar Sweden. A lokacin da take bayani darektar wasannin kwaikwayo ‚yar kasar Sweden mai suna Melanie Medelind ta ce rubuce-rubucenta na da burgewa saboda suna da saukin fahimta. Kuma a ko da yaushe ta kan yi tsokaci da siyasar kasar Austriya da dangantakarta da tarihin nahiyar Turai, musamman ma yakin duniya na biyu. A can Austriya dai akwai sabani a game da al’amuran Elfride Jellinek saboda yadda take bayyana ra’ayinta a fili. Marubuciyar adabin, wanda mahaifinta Bayahude ne dan usulin Chek, ba ta cikin rukunin ‚yan kasar Austriya dake rufa-rufa game da tarihin kasarsu. Kuma har yau tana fama da takaicin ganin cewar wasu daga al’umar kasar suna goya wa jam’iyyar nan ta Haider mai ra’ayin wariyar jinsi da kyamar Yahudawa baya. Tace ba zata yarda a yi amfani da ita wajen wanke sunan kasar Austriya daga wannan tabargaza ba.