1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

El baradei da hukumar IAEA sun lashe kyautar Nobel ta 2005

ibrahim SaniOctober 7, 2005

Hukumar Alfred Nobel dake birnin Oslo a kasar Norway sun bayar da sanarwar wadanda suka lashe kyautar nobel ta bana

https://p.dw.com/p/BvZ4
Mohd El baradei shugaban hukumar IAEA
Mohd El baradei shugaban hukumar IAEAHoto: dpa - Bildfunk

Kyautar nobel din dai ta bana za a raba tane a tsakanin Mohd El baradei da kuma hukumar da yakwa jagoranci wato hukumar dake lura da yaduwar makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA a turance.

Kyautar ta nobel ta wannan shekara na tattare ne da makuden kudade da yawan su ya tasamma miliyan goma irin kudin kasar Sweden, kwatankwacin miliyan daya da digo shidda ke nan na yuro.

A cewar shugaban alkalan dake gudanar da wannan zabe,wato Ole Danbolt Mjoes, an zabi El Baradei din ne da kuma hukumar da yakewa jagorancin bisa irin namijin kokarin da suka yi wajen hana yaduwar fasahar makamin na nukiliya a doron kasa.

A tsawon lokacin da yayi yana rike da wannan hukuma a cewar Ole Danbolt, Mohd El baradei ya dauki kwararan matakai na ganin cewa ba ayi amfani da fasahar ta wacce hanya ba da zata kawo barazana ga zaman lafiyar duniya.

Mohd El baradei dai dake a matsayin kwararren lauya daga kasar masar ya kasance yana jagorancin wannan hukuma ta IAEA a lokacin da ake fuskanci rikice rikice da rigingimu na zargin da akayiwa kasar iraqi da cewa tana kokarin kera makamin nukiliya, a waje daya kuma ga makamancin irin sa dake a kann kasashen koriya ta arewa da kuma kasar Iran.

A kuwa ta bakin kakakin hukumar ta IAEA wato Marc Viddricaire, cewa yayi babu shakka wannan sanarwa tazowa shugaban nasu da hukumasr ba zata domin basu taba zata ba.To amma duk da haka a cewar Marc wannan abu zai kara musu kwarin gwiwa naci gaba da aikin su yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin shugabannin kasashen duniya da kuma hukumomi naci gaba da tofa albarkacin bakin su game da wannan sanarwa ta wadanda suka lashe kyautar ta nobel ta wannan shekara.

Na farko daga cikin jerin mutanen akwai shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schroeder da shugaban kasar Faransa Jacques chirac da faraministan Biritaniya, Mr Tony Blair, wadanda dukkannin su suka nuna farin cikin su game da wannan zabe da hukumar Alfred Nobel din tayi da cewa ya dace.

A cewar shugabannin wannan zabe zai karawa hukumar ta IAEA da kuma shugaban nata kwarin gwiwar ci gaba da gagarumin aikin da suka sako a gaba na ganin cewa an samu kwanciyar zaman lafiya a doron kasa baki daya.

Bugu da kari sakataren Mdd wato Kofi anan shima ya tofa albarkacin bakin sa kamar haka: babu shakka wannan hukuma ta IAEA da shugaban nata El baradei sun yi rawar gani a don haka wannan kyauta da girmamawa ta dace dasu a dai dai wannan lokaci.

Haka shima tsohon sifeton bincike na mdd a iraqi wato Hans Blix da kuma na hannun daman shugaban kasar Russia wato Sergei prikhodko cewa suka yi an yi zabi na gari domin dukkannin su biyu sun cancanta, domin irin rawar da suke takawa waje samun kwanciyar zaman lafiya a duniya baki daya.

Shi kuwa tsohon faraministan kasar Israela kuma mataimakin na yanzu waton Shimon Perez cewa yayi wannan girmamawa da akayiwa IAEA da kuma El baradei ya dace to amma akwai bukatar shugabannin biyu suyi amfani da wannan dama wajen tursasawa mahukuntan iran kwance musu damarar da sukayi ta kokarin kera makamin nukiliya.