1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Edouard Philippe ya zama sabon Firaministan Faransa

Salissou Boukari
May 15, 2017

Kwana daya bayan da ya kama aiki, sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nada Edouard Philippe, a matsayin sabon Firaministan kasar jim kadan kafin ziyararsa ta farko da zai kai a kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/2czvI
Frankreich Bürgermeister Le Havre Edouard Philippe
Sabon Firaministan kasar Faransa Edouard PhilippeHoto: Getty Images/AFP/C. Triballeau

Dan shekaru 46 da haihuwa, sabon Firaministan na Faransa Philippe, baya daga cikin sabuwar jam'iyya ta "République en Marche" da ta kai Emmanuel Marcon a matsayin shugaban kasar ta Faransa, inda ake ganin hakan na daga cikin shirin sabon shugaban na hada kan 'yan kasar da kuma kokarinsa na ganin ya janyo 'yan jam'iyya mai ra'ayin mazan jiya domin samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokoki na watan Yuni mai zuwa.

Shi dai sabon fraministan na Faransa Philippe, na zama na kusa da Alain Juppe na jam'iyyar 'yan Repablicain da ta tsayar da Francois Fillon a matsayin dan takara a zagaye na farko na zaben na Faransa, amma kuma ta fuskanci rarrabuwar kanu dangane da tuhume-tuhumen da Fillon ya fuskanta a gaban masu bincike.