1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta karfafa dimukuradiyyarta

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
April 5, 2024

A kokarin bunkasa mulkin dimukuradiyya a tsakanin kasashe mambobinta, kungiyar Ecowas na shirin sauya yadda ake zabo ‘yan majalisar dokokin kungiyar daga nadi ya koma zabe domin ba da dama fada a ji a dimukuradiyyance.

https://p.dw.com/p/4eT8t
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Kokari ne na sauya tsarin da ake gani na nadi ya zuwa zabe bisa tafarkin dimukurdiyya domin sauya yadda kawai ake  nadi maimakon zabe ga ‘yan majalisar inda ake bai wa kowace kasa nata kason a tsakanin kasashen kungiyar 16 da ake da su, wanda masana a fanin dimukuradiya suke ganin ya saba wa tafarki na dimukuradiyya da aka gina a kan batu na zabe. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ta Ecowas ya ce babu yadda za a samu nasara ba tare da samun gardama da aiki tukuru na hukumomin majalisa ba, don haka domin cimma manufar kungiyar Ecowas nan da shekara ta 2050 suna bukatar sanya mutanen kasashensu a dukkanin shawarwarin da za a yanke.

Nigeria | ECOWAS-Staatsoberhäupter in Abuja 2023 | Regionale Zusammenarbeit
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Haka ma a cewar Tinubu, za a iya cimma wannan ne kawai ta hanyar zababbun wakilai wadanda bayan zama ‘yan majlisu a kasashensu, a zabo su zuwa majalisar dokokin Ecowas din.

Tun da farko shugaban hukumar Ecowas din  Dr. Omar Alieu Touray da ya jagoranci kaddammar da majalisar dokokin kungiyar, ya bayyana hali na koma bayan dimokurdiyya da ke fuskantar yankin saboda juye-juyen mulki da aka yi a wasu kasashe, inda ya bayyana sauya tsarin aikin majalisar a matsayin wanda zai yi tasiri.

A bisa tsarin da ake amfani da shi a yanzu, ana nada ‘yan majalisar ne daga majalisun dokoki na kasashen kungiyar inda ake rabawa a bai wa kowace kasa bisa ga yawan jama’arta.

Babu dai wakilci daga kasashen irin su Mali da Jamhuriyar Nijar da Burlkina Faso a majalisar dokoki ta shida ta Ecowas din da ta fara zamanta a Abuja baban birinin kasar Najeriya.