ECOWAS na shirin hukunta sojojin Nijar
July 30, 2023Akalla shugabannin yankin guda takwas ne dai suka taru a Abuja a Lahadin nan domin neman mafitar juyin mulkin da ke zaman barazana mai girma a cikin yankin Afirka ta Yamma. Wakilan kungiyar Tarayyar Afirka ta AU su ma sun halarci taron da ya tsayar da matsayar guda da nufin tilasta wa sojin Nijar din mayar da mulki ga Shugaba Bazoum Mohamed a cikin kwanaki bakwai.
Kungiyar ta ECOWAS ba ta tsaya a nan ba ta bukaci kasashe mambobinta su rufe iyakokinsu da Jamhuriyar Nijar a wani mataki na mayar da kasar saniyar ware domin matsa wa sojojin lamba su yi saurin sauka daga mulki.
Shugabannin ECOWAS din sun bukaci manyan hafsoshin soji na kasashe 15 da ke cikin kungiyar su yi wata ganawa ta gaggawa domin duba hanyoyin da za a bi wajen tunkarar sojojin Nijar idan har suka ki martaba wa'adin da ECOWAS din ta bayar.
''Shugaba Bazoum ne ke zaman halastaccen shugaba na jamhuriyar Nijar kuma duk wani mataki da ya dauka ko kuma na wakilin da ya nuna ne kawai kasashen ECOWAS za su mutunta.'' in ji Dr. Omar Tourey, shugaban hukumar gudanar ECOWAS
A bisa dukkanin alamu dai kungiyar ta ECOWAS ta fusata matuka da juyin mulkin karo na biyar da aka yi a Nijar tun bayan shekarar 1960, lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan Faransa. Bukatar da suka jadadda a taronsu na Abuja ita ce lallai sojojin Nijar su yi gaggawar sakin Shugaba Bazoum kuma su mayar masa da mulkinsa ba tare da bata lokaci ba. To amma babu tabbas ko sojojin za su martaba wannan kira.
Tun a gabanin taron na ECOWAS gwamnatin mulkin sojin ta Nijar ta aike wa da shugabannin na ECOWAS gargadin ka da wani daga cikinsu ko ma daga wajen Afirka ya kuskura ya yi musu katsalandan a abin da suka kira kokari na gyara kasarsu.