Iran: Zanga-zangar kin jinin gwamnati
February 24, 2023Duk da jami'an tsaron da aka baza tare da katse layin intanet da hukumomin kasar suka yi, zanga-zangar ta gudana a birinin da ke zama daya cikin cibiyoyin masu bore a kasar. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun wallafa faya-fayan bidiyon masu boren dauke da tutoci da allunan da ke dauke da kalaman batanci ga shugaban kasar Iran da suke kwatantawa da dan kama karya.
Sabuwar zanga-zangar dai ta biyo bayan mutuwar wani babban jami'in kiwon lafiya a lokacin da yake tsare a hannu jami'an tsaro bayan da aka zarge shi da laifin yin bore. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Iran ta ruwaito cewa 'yan sandan kasar na yin anfani da bindigogi wajen murkushe masu bore.
Idan za a iya tunawa akalla mutane 131 ne suka mutu tun farko fara boren kin jinin gwamnatin ta Iran bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini, lamarin da ya sa kasashen Yamma suka tsaurara wa Iran jerin takunkumai da suka aza mata.