1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mutane sun rasa rayukansu a girgizar kasa

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2023

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasar da ta auku a kasashen Turkiyya da Siriya ya hauru mutum dubu 4, a cewar sanarwar wannan safiyar.

https://p.dw.com/p/4NAyS
Türkei Iskenderun Erdbeben Krankenhauseinsturz Bergungsarbeiten
Hoto: Umit Bektas/REUTERS

A ci gaba da kai dauki ga mutanen da suka makale a baraguzan gini wadanda ibtila'in girgizar kasa ya rutsa da su a kasashen Siriya da Turkiyya, ya zuwa yanzu adadin wadanda suka rasa rayukansu a kasar Turkiyya na tunkarar mutum dubu uku yayin da a kasar Siriya suka haura mutum dubu da dari hudu.

Girgizar gasar mai maki 7.8 a ma'aunin Richter  na zama mumunar iftila'i da kasahen biyu suka fuskanta tun bayan makamanciyarta a shekarar 2000.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu, rahotanni sun tabbatar da jikkatar wasu da dama, kazalika an yi nasarar zakulo sama da mutum dubu takwas a jerin gini-gine da suka rushe.

Ko a safiyar wannan Talata an sake samun wata girgizar kasa a kudu-maso-gabashin Turkiyya. Tuni kasashen duniya suka fara neman hanyoyin da za su aike da taimakon su cikin gagawa.