1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban kananan yara a Afirka na fama da tamowa

Binta Aliyu Zurmi
January 12, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran agajin gagawa don ceto rayukan kananan yara miliyan 30 da ke fama da tamowa a wasu kasashen da ke fama da karancin abinci.

https://p.dw.com/p/4M6ET
Hungersnot am Horn von Afrika
Hoto: Zerihun Sewunet/UNICEF/AP Photo/picture alliance

Majalisar ta Duniya ta ce tashe-tashen hankula da fari da annobar corona gami da tsadar rayuwa sun bar kananan yara a kasashen Afirka sama da 15 a cikin hali na tsaka mai wuya.

Daga cikin kasashen da ake bukatar tallafi akwai Afganistan da Burkina Faso da Mali da Nijar da Najeriya Somaliya da Sudan ta Kudu da Yamen da sauransu.

Ana ganin idan har ba a magance wannan matsalar ba akwai yiwuwar ta'azzarar ta a wannan shekarar ta 2023. Taimakon zai maida hankali a kan kananan yara dake kasa da  shekaru 5 da mata masu juna biyu da matan da ke shayarwa.