SiyasaJamus
Jamus: Boren adawa da rigakafin corona
January 18, 2022Talla
Mutane sama da 70,000 sun yi zanga-zangar adawa da tilasta karbar rigakafin corona a Jamus. Zanga-zangar ta gudana a yammacin ranar Litininin a biranen Berlin da Rostock da Kolon da kuma Thuringia.
Hukumomi dai na daukar sabbin matakai ne domin dakile yadda corona musamman samfurin omicron ke ci gaba da yaduwa a kasar tamkar wutar daji. Sai dai bayanai sun ce a sakamakon yadda galibin mutane suka yi rigakafi, yawan masu kamuwa da omicron din bai sanya karuwar mace-mace a sanadiyar cutar sun yi tsanani ba a kasar ta Jamus.