Donald Trump ya nemi hadin kan 'yan adawa
February 6, 2019Shugaban Amirka Donald Trump ya yi kira ga majalisun kasarsa da su zartar da wata dokar ciniki wadda za ta rika yin ramuwar gayya wajen karbar haraji na kayayyakin da suke shigowa cikin kasar, kwatankwacin harajin da Amirka ke biya idan ta kai kayyakinta wasu kasashen. Shugaba Trump wanda ya yi wannan kira cikin babban jawabin shekara a zaman hadin gwiwa na majalisun dokokin Amirka, ya fara da tilawar nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru biyu, da suka hada da samar da karin masu yin aiki sama da milyan biyar, da rage haraji, da soke wasu dokokin da ke hana ruwa gudu, tare da jaddada cewa a halin yanzu Amirka ta bude wani sabon babi ta fuskar samar makamashi.
Ya ce " A yanzu Amirka ce a sahun gaba a jerin kasashen da suka fi samar da mai da iskar gas a duniya. "
Trump na son mayar da hankali kan ginin katanta da yakar cututtuka
Sauran batutuwan cikin gida da Shugaba Trump ya takalo sun hada da illolin rashin inganta matakan tsaro a iyaka ta kudanci, inda ya sake yin kira ga 'yan majalisa da su mara masa baya a kokarin da yake yi na yin katanga a iyakar Amirka da Mexico. Sannan ya jaddada wa dogarawan tsaron kasa wadanda ya ce a cikin shekaru biyu sun cafke bakin haure masu aikata laifuffuka dubu 266.
Da ya juya kan yaki da cututtuka kuma, Shugaba Trump ya yi alkawarin ci gaba da kashe makudan kudade wajen yaki da cutar HIV/AIDS, inda yake fatar binciken da za a ci gaba da gudanarwa, zai iya kawo karshen cutar a Amirka nan da shekaru goma. Kazalika, ya kuma koka dangane da yadda yara masu yawa ke fama da cutar sankara, watau cancer ko kuma cutar daji.
"A cikin kasafin kudin gwamnati, zan bukaci 'yan majalisa su ba da dala milyan 500 cikin shekaru goma nan gaba, da za a yi amfani da su wajen ci gaba da gudanar da bincike, da nufin ceto rayukan yaran da suke fama da irin wannan cuta. "
Da ya juya kan batutuwan kasashen waje kuma, kamar yadda aka yi hasashe, Shugaban na Amirka ya sake yin tilawar nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen matsa wa kasashen kungiyar kawancen tsaro ta NATO lamba suna sauke nauyinsu na bada gudumawa inda ya ce cikin shekaru biyu yanzu an samu fiye da dala bilyan dari daga kasashen don ayyukan na NATO. Ya kuma jaddada ci gaba da inganta sojojin Amirka su zarta kowa tare da jaddada cewa Amirka ba za ta taba zama kasa mai mulki irin na gurguzu ba.
Dangane da yake-yaken Afganistan da sauran matsalolin gabas ta tsakiya kuwa, Shugaban na Amirka ya ce kasashen da suka kasaita ba sa fafata yakin da ba a san karshensa ba. Trump ya ce a misali Amirka ta kashe sama da dala tiriloyin 7 a Gabas ta Tsakiya, ba tare da kawo karshen yakin ba. A dangane da haka ne ya ce gwamnatinsa ta kinkimi sabon salo don warware matsalolin Afganistan cikin siyasa, a daidai lokacinda aka kusa kakkabe kungiyar ISIS a Syriya, ana kusantar Koriya ta Arewa, don samun masalaha a yankin.
Trump ya sha caccaka daga 'yan adawa
Da take mayar da martani a madadin jam'iyyar adawa ta Democrats, Stacey Abraham, tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Georgia ta caccakki gwamnatin Trump dangane da rashin daidaitawa da majalisa wanda ya haddasa rufe wasu ma'aikatun gwamnatin tsawon kwanaki 35.
Ta ce "Duk da cewa mai yiwuwa muna da bambamcin ra'ayin siyasa, amma ba zai yiwu mu sabatta amanar da muka yi ba game da kyawawan akidun kasar nan. "
Yanzu haka ra'ayoyi sun sha bamban, inda wasu ke ganin cewar furucin neman hadin kai da Shugaba Trump zai iya taimakawa wajen inganta dangantarsa da Democrats, yayin da wasu kuma suke cewa za a ci gaba da turanci a sauran shekaru biyu na mulkin Trump.