Desmond Tutu ya rasu yana da shekaru 90 a duniya
December 26, 2021Fitaccen malamin addinin Kirista wanda ya yi yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu Archbishop Desmond Tutu ya rasu. Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da mutuwar tasa a safiyar wannan Lahadi, inda ya ce marigayin ya kasance mai kokarin ganin an samu daidaito a tsakanin al'umma. Tutu mai shekaru 90 a duniya dai ya mutu a wani asibiti da ke birnin Capetown. Sai dai iyalansa da su ma suka tabbatar da mutuwar ta malamin addinin ba su bayyana cutar da ta yi ajalinsa.
A lokacin rayuwarsa ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a sakamakon fafatukar da ya nuna ta lumana wurin kare 'yancin bakaken fata da a baya fararen fata tsiraru ke muzguna musu. Ya yi wannan aiki tare da amininsa Nelson Mandela wanda wannan bukata ta ja masa zaman kaso na shekaru 27.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson tuni ya wallafa sakon ta'azziyya a shafinsa na Twitter, inda ya ce za a rika tunawa da dattakon da Archbishop Desmond Tutu ya rayu da shi na tsawon shekaru.