1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dawowar 'yan tawayen M23 a Kwango

Suleiman Babayo MA
April 7, 2022

Bayan tsagaita wuta na kusan shekaru 10, 'yan tawayen kungiyar M23 a Kwango sun kai hari yankin gabashinta inda dubban fararen hula suka tsere zuwa kasar Yuganda.

https://p.dw.com/p/49bj1
Mai-Mai Milizen im Kongo
Hoto: Dai Kurokawa/dpa/picture alliance

An kwashe shekaru a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cikin kwanciyar hankali, kafin kwanakin da suka gabata kungiyar 'yan tawaye mai karfi ta M23 ta kai hari kan sojojin kasar kusa da iyakar kasashen Yuganda da Ruwanda.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashin hankalin ya raba dubban mutane da gidajensu, inda wasu suka tsere zuwa garin Goma fadar lardin arewacin kasar, sannan wasu sun tsallaka iyaka zuwa kasar Yuganda.

Rundunar sojan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta tabbatar da kai harin ta kuma zargi sojojin Ruwanda da taimakon 'yan tawayen na kungiyar M23. Tuni gwamnatin Ruwanda da 'yan tawayen suka musanta zargin.

Mai-Mai Milizen im Kongo
Hoto: Dai Kurokawa/dpa/picture alliance

Bayan shafe kwanaki ana musayar wuta, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin, kuma kungiyar ta M23 ta ce tana bukatar tattaunawa da gwamnatin shi ya saka ta janye mayaka daga yankunan da aka yi gumurzu. An kafa kungiyar M23 a shekara ta 2012 bayan rusa wata rundunar mayaka inda aka saka hannu kan yarjejenyiar zaman lafiya. Tsoffin mayakan sun zargi gwamnati da rashin cika alkawari.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce cikin wannan shekara kimanin mutane 2,300 suka rasa rayukansu a tashe-tahsen hankula na gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango.