SiyasaTurai
DAVOS: Ukraine ta jaddada bukatar shiga NATO
January 16, 2024Talla
Yayin da ministan harkokin wajen Saudiyya ya caccaki Isra'ila a taron tattalin arzikitattalin arziki na duniya wato Davos da cewa, tana jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin hatsari, shi kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya jaddada bukatar shiga kungiyar tsaro ta NATO a wannan shekara ta 2024.
Zelensky, ya sanar da sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, cewar yana bukatar kungiyar ta gaggauta daukar mataki a wannan shekara na matso da muradun Ukraine shiga kungiyar.
Ya kuma bayyana halin da kasar ke ciki a yakin da suke fafatawa da Rasha, tare da bukatar karin tallafin kayayyakin yakin soji ga Ukraine musamman domin maida martani kan hare-haren Rasha ta sama a wasu sassan kasar.