Hukuncin kan kisan shugaban kasa
March 21, 2023Talla
A wannan Talata kotu a kasar Chadi ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga 'yan tawaye fiye da 400 da ake zargi da kisan tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno a shekara ta 2021. Mai gabatar da kara na gwamnati ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP haka.
Shi dai mai gabatar da kara Mahamat El-Hadj Abba Nana bai yi karin haske ba kan daurin, amma ya ce akwai wasu mutane 24 da aka sake.
Shi dai Marigayi Idriss Deby Itno shugaban kasar Chadi ya rasa ransa lokacin artabu tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye da suka kunno kai daga kasar Libiya mai makwabtaka. Kuma tun lokacin aka nada dan-marigayin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban kasra ta Chadi.