1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka tsakanin Rasha da China

Abdullahi Tanko Bala
May 24, 2023

An rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Rasha da China tare da kulla kawancen tattalin arziki

https://p.dw.com/p/4Rlum
Shugaban China Xi Jinping da Firaministan  Rasha Michail Mischustin
Hoto: Huang Jingwen/Xinhua News Agency/picture alliance

Rasha da China sun sanya hannu a kan wasu yarjeniyoyin tattalin arziki a daidai lokacin da kasashen yamma ke sukar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yayin da yakin Ukraine ke kara tsawaita.

Firaministan Rasha Mikhail Mishustin wanda ya kai ziyara China ya tattauna da Firimiya Li Qiang zai kuma gana da shugaba Xi Jinping

Mishustin ya shaida wa Firiminiyan China cewa dangantakar da ke tsakanin Rasha da China ta kai wani matakin kololuwa da ba a taba tsammani ba, na mutunta juna da martaba muradun kowa da kuma tunkarar kalubalen siyasar duniya da matsin lamba daga gamaiyar kasashen yamma.

A nasa bangaren Li ya baiyana kawancen da ke tsakanin China da Rasha da cewa wani sabon karni ne.

Yarjejeniyar da suka rattaba wa hannu ta kunshi fannin cinikayya da safarar kayan amfanin gona zuwa China da kuma fannin wasanni tare da yarjejeniyar fahimtar juna.