1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ganawa tsakanin Trump da Kim

Suleiman Babayo LMJ
April 30, 2018

Ana kara samun haske game da shirin Koriya ta Arewa na rufe wuraren inganta makaman nukiliya bayan ganawa da aka yi tsakanin shugabannin kasashen na Koriya ta Arewa da ta Kudu

https://p.dw.com/p/2wwOv
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa na Amirka Donald Trump
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa na Amirka Donald TrumpHoto: picture-alliance/AP/dpa/Wong Maye-E

Lokacin da aka tarbi Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu yayin taron majalisar gudanarwa ta kasar, bayan taron da ya wakana a makon jiya tsakanin shugaban na Koriya ta Kudu da kuma takwaransa Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa. Shugaban na Koriya ta Kudu ya ce tuni ya samu goyon baya bisa yunkurin saka Koriya ta Arewa cikin jerin kasashen duniya, idan ta yi watsi da shirin makaman nukiliyarta. Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu ya kara da cewa:

Trump ya taka rawa a kawo karshen rikicin Koriyoyin biyu

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-inHoto: Reuters

"Musamman Shugaba Donald Trump na Amirka wanda ya nemi kawo karshen yakin Koriya kuma ya duba yanayin da ake ciki da taron kasashen Koriya, domin samun zaman lafiya da bunkasa. Amma mataki na farko kawai aka dauka a mastayin mafari. Kasashe makwabta na China da Japan da Rasha gami da sauran kasashen duniya sun yi maraba da wannan taro tare da goyon bayan haka."

Tuni gwamnatin ta Koriya ta Kudu ta dauki matakin janye nu'urorin amsa kuwa da ta saka wadanda ke yada farfaganda zuwa Koriya ta Arewa daga kan iyakar kasashen biyu. John Bolton mai ba da shawara kan fannin tsaro ga Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce wata kila a samu nasara cikin hanzari na dakile shirin nukiliyar Koriya ta Arewa kamar yadda aka gani a kasar Libiya a baya. Ana ganin tattaunawar da ake tsarawa tsakanin Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa da Shugaba Donald Trump na Amirka za ta mayar da hankali kan watsi da shirin nukiliyar Koriya ta Arewa, samun tabbacin rashin kai wani farmaki zuwa Koriya ta Arewa da janye takunkumin karya tattalin arziki da ke kan kasar ta Koriya ta Arewa. 

Nordkorea Raketentest in Pjöngjang
Gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi.Hoto: Getty Images/AFP/STR

Koriya ta Arewa ta fara daukar matakai

Gwamnatin ta Koriya ta Arewa tuni ta fara nuna cewa da gaske take yi a wannan karo ta hanyar cewa za ta rufe tashar binciken nukiliya ta kasar cikin watan Mayu mai kamawa, gami da dai-daita lokacin agogo tsakanin Koriyoyin biyu kamar yadda tashar talabijin ta kasar Koriya ta Arewa ta yada. Daga ranar biyar ga watan gobe na Mayu Koriya ta Arewa za ta gyara agogon kasar domin tafiya tare da na Koriya ta Kudu. A kokarin tabbatar da zaman lafiya a mashigin ruwan Koriyan, ministan harkokin wajen China Wang Yi zai kai ziyara zuwa Koriya ta Arewa ranakun Laraba da Alhamis masu zuwa.