Dan takara a zaben Jamus ya soki Merkel kan Turai
August 18, 2013Peer Steinbrueck dan takaran zama shugaban gwamnati karkashin babbar jam'iyyar adawa ta SPD, ya bayyana wa wani babban gamgamin yakin neman zabe cewa, shirin Merkel da jam'iyya mai mulki na CDU na shafan Jamus da sauran 'yan kasashen Turai da ke cikin matsalolin tattalin arziki, saboda yadda ta nemi zabtare kasafin kudi, maimakon neman hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
Steinbrueck ya kasance ministan kudi yayin wa'adin mulkin Angela Merkel na farko daga shekara ta 2005 zuwa 2009, karkashin babbar gwamnatin kawance.
Ranar 22 ga watan gobe na Satumba Jamusawa za su kada kuri'ar tantance makomar kasar, inda 'yan siyasa ke ci gaba da karakaina cikin lungu da sakon kasar, domin samun goyon bayan kaiwa ga madafun iko.
Mawallafi: AFP/Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu