Dan jaridar Saudiyya ya yi batan dabo
October 4, 2018Ofishin ministan harakokin kasashen wajen kasar Turkiyyar dai ya sanar da cewa dan jaridar mai shekaru 59 da ya yi batan dabo sama da awoyi 24 da suka gabata, na a cikin ofishin jakadancin kasar Saudiyya a birnin Istanbul inda ya je domin gyaran wasu takardu.
To sai dai mahukuntan Saudiyyar sun bayyana cewa dan jaridar da ke yi wa jaridar Washington Post aiki ya fita daga ofishin jakadancin kasar da ke a birnin na Istanbul. Yanzu haka dai karamin ofishin jakdancin Saudiyya a Istanbul ya sanar da soma aikin bincike tare da mahukuntan birnin Istanbul domin gano yadda aka yi wannan dan jarida ya yi kasa ko bisa.
A shekarar da ta gabata ce Jamal Khashoggi ya yi gudun hijira zuwa kasar Amirka a bisa tsoran kamu bayan da ya soki lamirin matakin yarima Mohammed Ben Salmane na kai hari a kasar Yemen.