An soki matakin fifita Ukraine
September 24, 2022Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na daga cikin wadanda suka ja hankalin taron Majalisar Dinkin Duniya kan rigingimu masu tayar da hankali da ke gudana, inda ya bayar da misali da rikicin Isra'ila da Falasdinu da kuma halin kuncin da 'yan kabilar Rohingya sama da miliyan daya ke ciki, Shugaba Buhari ya ce, yakin Ukraine shakka babu wani tashin hankali ne da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu sai dai duk da haka kada a mance da sauran yankunan da ke fama da tashe-tashe hankula da ke bukatar taimako da dace suma a tausaya musu. Furucin shugaban a taron majalisar na birnin New York a Amirka ya haifar da guna-guni a zauren taron.
Alkaluman ofishin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu sun hada sama da dala biliyan uku da rabi don taimakawa Ukraine da 'yan gudun hijirarta tun bayan barkewar yakin watannin bakwai da suka gabata, amma dala biliyan biyu kadai aka iya samar wa Yemen da mutane fiye da miliyan 17 ke fama da matsananciyar yunwa bayan shafe fiye da shekara goma ana yaki a kasar.