Dambaruwar majalisa kan tsarin zaben Najeriya
April 19, 2018Watsi da dagewa a kan sauya jadawalin zaben Najeriyar dai abu ne da ya kawo ja-in-ja da ma kai ruwa ranar da aka fuskanta a kan wannan batu. Domin tun daga lokacin da majalisun suka sauya tsarin da nufin a fara gudanar da zabensu sannan a yi na shugaban kasa a karshe, an dai kai ruwa rana da ma raba majalisar gida biyu a tsakanin masu goyon baya da masu adawa. Ko me suka hango a yanzu suka yi watsi da daukacin lamarin. Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na cikin wadanda suka yi muhawara tare da amincewa da komawa tsarin da ake da shi.
A bisa tsarin da aka amince da shi tare da tura shi zuwa ga kwamitocin majalisun biyu, an tsara za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, sannan sai a yi na gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki. Bisa wannan tsari za'a yi zabubbuka biyu maimakon guda uku da suka so a yi. Wannan ya sanya Hon Sidi Yakubu Karasuwa na majalisar wakilan Najeriyar bayyana muhimmancin wannan ga demokradiyyar Najeriya. Tun kafin wannan mataki shugaban Najeriya ya ki sanya hannu a sauya tsarin da aka yi, a yayin da ake muhawarar halacci da ikon yin haka ga majalisar, domin hukumar zaben kasar ta dage kan cewa ita ce ke da ikon sanya tsari da ranakun zabe.