Damaturu ya koma hannun jami'an tsaro
December 1, 2014Hukumomi a jihar Yoben Najeriya, sun tabbatar da cewa jami'an tsaron Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram daga birnin Damaturu, bayan wani hari da 'yan bindigan suka kai da farar safiyar yau Litinin, da ya sanya jama'ar gari masu yawan gaske kauracewa birnin.
Gwamnan jihar ta Yobe Ibrahim Gaidam, ta bakin kakakin sa Abdullahi Bego, ya yi Allah wadai da harin, sannan ya yabawa tsayin daka da jami'an na tsaro suka yi wajen fatattakar maharan.
Malam Abdullahi Bego ya ce a halin da ake ciki jami'an tsaro ne ke rike da Damaturu babban birnin jihar cikin wata hira da DW, da ranar yau:
"Da misalin karfe biyu da rabi agogon Najeriya, bayanin da muke da shi, shi ne, tabbas jami'an tsaron Najeriya, da sojoji da 'yan sanda da jami'an tsaro masu farin kaya, sun fatattaki wadannan mahara, kuma a yanzu haka suna cigaba da fatattakarsu. Gaba daya Damaturu yana hannun jami'an tsaro ne, sannan kuma wadanda suka buya ana binsu a lungu-lungu ana bincikawa"