Sabon salon koyar da almajirai a Nijar
June 9, 2020Talla
Wanan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da sannu a hankai hukumomi da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke bankado ta'asa da aika-aikar da ke faruwa ga wasu almajirai a makarantun tsangaya, musamman wadanda ake turawa ci-rani a tsakanin Jamhuriyar ta Nijar da kuma makwabciyarta Najeriya.
Lamari na baya-bayan nan shi ne na jihar Diffa, inda a yanzu ya mamaye shafukan sada zumunta na zamani. Shugaban kungiyar makarantun allo ta kasa UECN, Malam Mahamadu Ibrahim ya ce tuni kungiyar tasu ta dauki mataki kan wannan matsala.
Ana iya cewa dai, ya zuwa yanzu dai fargabar da mutane ke ji suke kuma gani daga nesa ta fara kwankwasa masu kofa, ganin yadda a jihar Diffa aka cafke wani malami da ke cin zarafin almajirai.