1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Yemen sun hallaka 'yan Al-Qai'da

Englisch-redJune 4, 2012

Rundunar sojin Yemen ta ce dakarunta sun samu nasarar hallaka 'yan ƙungiyar Al-Qaida guda ashirin da daya a wasu laduna da ke kudancin ƙasar a jiya lahadi.

https://p.dw.com/p/157OR
A defected army soldier supporting protestors looks on from behind a weapon mounted on a patrol truck to secure a street where protestors demand the trial of Yemen's former President Ali Abdullah Saleh, in Sanaa, Yemen, Friday, March 30, 2012. (Foto:Hani Mohammed/AP/dapd)
Jemen MilitärHoto: dapd

Rundunar dai ta ce sha uku daga cikin 'yan ƙungiyar ta Al-Qa'idan sun gamu da ajalinsu ne yayin wata taho mu gama da su ka yi da su a wajen garin Jaar.

Wani daga cikin jami'an sojin ƙasar ta Yemen da ya buƙaci manema labarai su sakaya sunansa ya ce dakarunsu sun hallaka 'yan Al-Qa'ida shidda a garin Abyan da ke zama fadar mulkin Zinjibar a jiya lahadi.

'Yan ƙungiyar ta Al-Qaida dai sun karbe iko da akasarin kudancin ƙasar ta Yemen a daidai lokacin da 'yan ƙasar su ka fantsama kan tituna don gudanar da boren ƙin jinin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar ta Yemen Ali Abdallah Saleh a shekarar da ta gaba, lamarin da ya sanya dakarun gwamnati ke ta ɗauki ba daɗi da su wajen ƙwato wannan yankunan da su 'yan Al-Qai'dan su ka ƙwace su ke kuma cin karensu ba babbaka.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal