Dabarun matan Sudan na kauce wa fyade
September 19, 2023Matan Sudan na samun horo a daya daga cikin sansanonin da ake wa lakabi "Mata masu taya sojojin Sudan yaki" da aka bude a birnin Nyalah, inda ake zargin kungiyar RSF da yi wa daruruwan mata fyade. Hindu Uthman daya daga cikin mata masu fafutuka da suka kafa wannan sansani ta ce: "‘Galibin matan da ake wa fyade 'yan shekaru 12 zuwa 18 ne da ba su san me tarzoma da tashin hankali ba. Irin wadannan 'yan matan na fuskantar cin zarafi da bacewa, don haka ne muka amsa kiran Shugaba al-Burhan na taimakawa."
Karin bayan: #Laberiya: Maza na fafutukar yaki da fyade
Baya ga koya wa matan dabarun yaki da harba bindiga gami da taimakon gaggawa ga masu raunuka da dabarun rarrashin jarirai da yara kananan da suka firgita, an ware wasu sansanoni na daban da ake koya musu nau´o´in fadace-fadacen da ake daukarsu a wasu lokutan a matsayin wasannin motsa jiki, kamar fadan takwendo da dambe da kokawa. Salma Idris da ke ba wa matan na Sudan horo ta ce yin hakan,na daya daga cikin hanyoyin kare mutuncin mata.
Yusrah Ma`amoun da aka yi wa fade ta ce ta yi ammanar cewa, da ace ta koyi dambe a baya, da wanda ya yi mata fyaden ya dandana kudarsa: "‘Na rungumi kaddara na fita daga cikin halin zaman bakin ciki bayan da na fahimci cewa, damuwa na sa a kara kiba da jangwabewa. A yanzu nauyina ya ragu, jiki na yayi daidai. Na san makasar makiya da zan iya yi ma kwaf daya idan ya tunkare ni, albarkacin horon da na samu kan wannan wasan damben."
Karin bayani: #Zargin cin zarafin mata da yara a gidan yarin Maiduguri
Ana dai nuna fargabar kan yiwuwar irin wadannan sansanoni koya wa mata horon kare kawunnasu su zama wuraren da masu yaki da za su dinga kai wa hare- hare.