Wani dan China ya mutu a Paris da ciwon Coronavirus
February 15, 2020Talla
Ministan kiwon lafiya na Faransa a wani taron manema labarai da ya kira ya ce wani dan yawan bude ido dan Kasar China da ke yIn jinyar cutar tun cikin wata Janairu ya mutu a wani asibiti da ke a Paris. Wannan shi ne karon fari da wani wanda ke fama da cutar ta Coronavirus ya mutu a nahiyar Turai. Ciwon na Coronavirus da ke shafar numfashi wanda aka gano a cikin watan Disanmba a lardin Hubei na China yanzu haka ya kashe mutane 1550 a Chaina kana wasu dubu 66 suka kamu da shi.