1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar kule a Koriya ta Arewa

Abdourahamane Hassane
May 12, 2022

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya ba da umarnin daukar matakan kulle a duk fadin kasar bayan da aka gano wasu mutanen na farko da ke dauke da kwayoyin cutar Covid 19.

https://p.dw.com/p/4BAVD
Nordkorea | Omicron-Variante | Der nordkoreanische Machthaber Kim Jong-un
Hoto: Yonhapnews Agency/picture alliance

Wannan shi ne karo na farko da aka samu bullar cutar a Koriya ta Arwewa sama da shekaru biyu bayan bazuwar annonbar a duniya wacce a yanzu da sannu a hankali aka fara samun saukinta a cikin sauran kasashe. Wasu gwaje-gwajen da aka gudanar a birnin Pyongyang daga masu fama da zazzabi ya zo daidai da nau'in cutar na corona na Omicron BA.2 mai saurin yaduwa. Kwararru sun ce tsarin kiwon lafiyar Koriyan da ke da kura-kurai ,zai wahala wajen tinkarar cutar, musamman ma ganin cewar a kasar babu wanda aka yi wa allurar rigakafi cikin mutum miliyan 25.