1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta gyara asibitoci don yaki da Covid-19

April 4, 2020

Gwamnatin Najeriya ta sanar a wannan Asabar cewa ta bude asusun tara kudi da suka kai Naira milyan 500,000 domin daukaka darajar asibitocinta don yaki da coronavirus. 

https://p.dw.com/p/3aSuG
Nigeria Geldwechsler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Gwamnatin kasar ta fitar da wannan matsaya ce bayan wani taro da aka gudanar a tsakanin Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmed da Shugabannin Majalisun Dokokin kasar. Gwamnatin ta ce za a samu wani kaso na kudaden daga aljihun gwamnati. Za kuma a samu tallafi daga kasashen ketare da kuma basussuka. Hukumomi sun yi amannar cewa wannan tsari zai ba su damar tunkarar annobar corona yadda ya kamata. 

A makon da ya gabata ma dai Babban Bankin Najeriya ya jagoranci tara kudade daga wurin attajiran kasar da suka kai Naira milyan 120,000 domin dai a yaki corona wace kawo yanzu ta kama 'yan kasar guda 210 ciki kuwa har da gwamnoni guda uku da babban jami'i a fadar shugaban kasar.