1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta bude taron duniya kan sauyin yanayi

November 6, 2022

Ambaliyar ruwar da aka yi Pakistan da Najeriya da karancin ruwan saman da aka fuskanta a Afirka gami da annobar guguwa dabam-dabam a kasashen Caribean na daga cikin abubuwan da wannan taro zai fuskanta.

https://p.dw.com/p/4J7ov
Ägypten | UN-Weltklimakonferenz COP27 in Scharm el Scheich
Yadda aka bude taron COP27 a MasarHoto: Gehad Hamdy/dpa/picture alliance

An bude babban taron MDD kan sauyin yanayi da aka yi wa lakabi da COP27 a kasar Masar. Wannan taro shi ne karo na farko tun bayan da rikicin Rasha da Ukraine ya sauya duniya.

A yayin jawabinsa na mika ragamar COP27 daga hannun Birtaniya zuwa kasar Masar, shugaban da ya jagorancin taron sauyin yanayin da ya wuce a Birtaniya Alok Sharma, ya ce wajibi ne shugabannin duniya su tashi tsaye domin tunkarar kalubalen sauyin yanayin da ke kara bunkasa a doron kasa. Taron dai zai gudana ne daga wannan Lahadi zuwa ranar Jumma'a 18 ga watan Nuwamba.