Matasa na fusknatar cin zarafi a kafar intanet
April 5, 2023Matasa da dama a kasar Afirka ta Kudu suna cikin mawuyacin hali sakamakon irin wannan cin zarafi. Babu wanda ya tsira daga hakan. Lamarin na ci gaba da zama barazana ga lafiyar kwakwalwar matasa masu amfani da intanet. Irin abin da ke faruwa ya shafi karatun 'yan makaranta inda wasu ba sa samun jarabawa mai kyau saboda tunanin abin da ke faruwa. Wani kiyasi ya nuna kashi 54 cikin 100 na iyaye a kasar Afirka ta Kudu suna sane da cewa 'ya'yansu suna fuskantar cin zarafi a kafar intanet. Lamarin ya ta'azzara a makarantu, amma babu wani abin da iyaye za su iya yi domin tsayar da hakan.
Duk da haka hukunta masu cin zarafin na da wuya, tun lokacin da aka samu habakar intanet da kafofin sada zumunta a nahoyar Afirka, haka ya shafi rayuwar al'ummomi daga duk bangarorin rayuwa, da shekaru. A kasashe da dama cin zarafin ta intanet ba laifi ba ne, kamar a kasar Afirka ta Kudu.
Mutum sai dai ya dauki hanyar kare kansa. Kuma an samu wani matashi daga Najeriya mai suna Joshua Agboola wanda ya nakalci na'ura mai kwakwalwa da yake da shafi a kafar YouTube. Ganin yadda shafi intanet yake da girma wajen samun bayanai masu tarin yawa, matashin yaron Joshua Agboola ya kirkiri hanyar da yara za su kare kansu. Wannan mataki na farko na samun nasarar da ake bukata daga matsalolin cin zarafi da ake fuskanta a kafar ta intanet.