1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050210 Auslandskorrespondenten Bundesregierung

February 4, 2010

Har yau dai ana fama da kai ruwa rana tsakanin jam'iyyun gwamnatin haɗin guiwar Jamus da ta cika kwanaki 100 da kafuwa

https://p.dw.com/p/Lsj4
Angela Merkel 'yar CDU da Guido Westerwelle ɗan FDPHoto: DW-Montage/picture alliance/dpa

A yau ne gwamnatin haɗin guiwa ta 'yan mazan-jiya da masu sassaucin ra'ayin siyasa a nan Jamus suka ta samu kwanaki 100 da kama ragamar mulki. To sai dai kuma a cikin waɗannan kwanaki talatin an sha fama ne da saɓani tsakanin sassan biyu ba ma tare da tsoma bakin 'yan hamayya ba. Har yau jam'iyyun na 'yan Chritian Union da Free Democrats suna ci gaba ne da lalube a cikin duhu a ƙoƙarin neman alƙiblar da zasu fuskanta. To ko yaya manema labarai na ƙetare dake aiki a Berlin suke kallon lamarin.

A wani lokacin dai waiwaya daga waje kan zama tamkar madubi, kuma irin wannan madubin ba zai iya daɗaɗa wa gwamnatin haɗin guiwa ta 'yan Christian Union da Free Democrats ba. Ga dai ra'ayin wasu daga cikin manema labarai na ƙetare dake gudanar da aikinsu a fadar mulki ta Berlin.

"Yau dai an samu kwanaki ɗari cir da kafa wannan gwamnati, kuma a ganina tana tafiyar da ayyukanta ne kamar yadda aka saba yau da kullu."

"Kawo yanzun dai ba wani abin a zo a gani da gwamnatin ta aiwatar/ Ba wata takamaimiyar alƙibla da ta fuskanta, ba wata tsayayyar shawarar da aka gabatar. Komai ya tsaya ne cik."

Wannan dai shi ne ra'ayin da yawa daga cikin manema labarai dake aikewa da kafofin yaɗa labarai na ƙetare rahotanni daga birnin Berlin dangane da gwamnatin haɗin guiwar Jamus 'yar kwanaki 100 da kafuwa. Aqsam Sulaiman, shugaban ofishin gidan tejebijin na Aljazeera dake Berlin ya ce tuni al'amura suka kai masa iya wuya a game da harkar gwamnatin ta haɗin guiwa. Ya kuma ƙara da cewar:

"A haƙiƙa sannu a hankali na fara goyan bayan ra'ayin kaka ta dake cewar ba kowane aure ne da aka yi akan soyayya ke ɗorewa fiye da auren tilas ba. Irin wannan auren ko da yake yana da ban sha'awa, amma fa ba'a daɗewa sai al'amuran rayuwa ta yau da kullum su fara rutsawa da shi, ta yadda maganar soyayyan ma za a wayi gari ta sha ruwa."

Shi kuwa Ahmet Külatschi, babban mai aikewa da jaridar Hürriyet ta ƙasar Turkiyya rahotanni cewa yayi sabuwar gwamnati na fama giɓi a tsayayyun manufofi na siyasa. Babban misali a nan shi ne dokar taɗa komaɗar tattalin arziƙin da aka amince da ita baya-bayan nan. Gabatar da dokar ta sassaucin haraji da taimakon iyali ke da wuya, sai aka fara ɓaɓatu kanta. Ya kuma ce:

"Abin dai na da ban mamaki. Domin kuwa idan har mutum ya amince da abu, ke nan ba abin da ya rage illa ya wanzar da shi. Amma sai ga shi hakan bai faru ba. A sakamakon haka martabar gwamnatin a halin yanzu dai ta zube a manufofinta na cikin gida."

Amma Dmitri Tultschinski daga kamfanin dillancin labaran Rasha na Rianovoosti, ra'ayinsa ya banbanta. A ganinsa duk da famar kai ruwa ranar da ake yi akan maganar haraji da kiwon lafiya da matsalar sojojin Jamus a Afghanistan, wannan ba abu ne da ya saɓa wa al'ada game da ayyukan gwamnati ba.

Ɗan jaridar Amirka Mathew Karnitschnig dake aikawa da jaridar Wall Street rahotanni yana tattare ne da ra'ayin cewar wannan saɓanin na mai yin nuni ne da buƙatar dake akwai game da canjin yanayin siyasar Jamus. A ganinsa kamata yayi manyan jam'iyyun siyasar ƙasar su fara tunani game da sabbin abokan haɗin guiwa, inda misali 'yan Christian Union zasu amince da yin haɗin guiwa da jam'iyyar The Greens, sannan ita kuma Social-Domocrats ta yarda ta shiga haɗin guiwa da 'yan kwaminis.