Cigaba da zaman sojin Amirka a Afghanistan
September 30, 2014Talla
Cikin yarjejeniyar dai sojin Amirka tare da na kungiyar kawancen tsaro ta NATO su dubu 10 za su kasance a Afghanistan din don bada horo da shawarwari ga sojin kasar bayan karewar wa'adin zamansu a ranar 31 ga watan Disamban da ke tafe.
Shugaban kasar Asraf Ghani ya ce wannan yarjejeniya da suka sanyawa hannu na nuna irin cigaba mai ma'ana da kasar ta fara samu dangane da irin dangantakar da ta ke da shi da kasashen duniya, kana yarjejeniya za ta taimakawa sha'anin tsaro da dorewar kasar baki daya.
A baya dai tsohon shugaban kasar Hamid Karzai ya ki sanya hannu kan wannan yarjejeniya duk kuwa da irin bazanar da Amirka ta yi na janye dakarunta baki daya.