Ci-gaban zanga zanga a Yemen
December 26, 2011Duban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Yemen domin nuna damuwar su dangane da mutuwar jama'ar da aka samu har guda tara masu adawa da gwamnatin Ali Abdallah Saleh a a lokacin wata zanga zanga .Duk da kiran da mataimakin shugaban ƙasar ya yi Abed Rabbbo Mansur na a ƙwantar da hankula ;yanzu haka masu gudanar da boren na buƙatar da ya sauka da ga kan karagar mulki tare da hukumta waɗanda ke da hannu a cikin kisan na jama'a.Ali Abdallah Saley wanda ya ƙwashe kusan shekaru 33 a kan mulki .
Daga bisani a cikin watan nuwanba da ya gabata ya amince ya miƙa mulki ga mataimakin sa har lokacin da za a shirya zaɓen shugaban ƙasa na kafin wa'adi a shekara ta 2012.Kana kuma shugaba Saleh ya ce zai ficce daga ƙasar ,'''ya ce zan je Amurka na yi magani kuma ina son na ba da wata sa'a ta shirya zaɓe ga ƙasa ta.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu