1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban shara'ar tsohon shugaban Masar

January 6, 2012

Bayan sunyi ƙwanaki uku a jere suna gabatarwa alƙalai da dalilai da shaidinsu,daga ƙarshe dai,masu gabatar da ƙara na ƙasar Masar sun nemi da a yanke hukuncin rataya ga Hosni Mubarak.

https://p.dw.com/p/13ffM
Ägypten Prozeß gegen Hosni Mubarak wird fortgesetzt in Kairo Krankenbett
Hosni Mubarak Tsohon shugaban ƙasar MasarHoto: Reuters

Wannan shara'a da yan ƙasar ke yi wa taken da shara'ar ƙarni, itace irin ta ta farko a tarihin ƙasashen larabawa a duniyar yau,ta jawo tada jijiyoyin wuya tsakanin lauyoyi masu gabatar da ƙara da waɗanda ake tuhuma.A ta bakin masu gabatar da ƙara,nauyin kashe kashe da aka yi wa masu zanga zanga ya rataya kan shugaban ƙasar ƙasar,gami da shiru da yayi yana ganin ana kisa.Batun da muka gabatarwa alƙalan,ba wai kawai maganar fatar baki bace,da ke sosa rai, ,hujjoji ne da ke nuna rashin imanin shugaban da ministan cikin

Su kuwa lauyoyin wanda ake tuhuma,sun dage kan cewa,babu wani rubutaccen umarni daga shugaban dake bawa jami,an tsaro izinin yin amfani da ƙarfin da ya wuce kima kan masu zanga zangar,suna masu aniyar daga ƙara karan har alƙalan suka yanke hukuncin..

Mubarak na iya fuskantar hukumcin rataye wa

A wajen kotun kuwa,dangin wadanda suka rasa rayukansu,sunyi ta daga kwalaye suna kira da a gaggauta zartar da hukuncin.Mi ake jira,har yanzu,ai maza maza a yanke hukunci"Su kuwa wasu dake ƙaunar shugaban,cewa suke,kiraye kirayen zartar masa da hukuncin ratayewar,butulci ne ga shugaban,bayan da ya yi fiye da shekaru hamsin yana bautawa ƙasar,da kuma kasan cewarsa kwamandan sojojin sama,da ya sadaukar da ransa,ya kuma taka gagarumar rawa, yayin yaƙin da ƙasar ta yi da isra,ila a shekarar Alif dubu daya da ɗari tara da saba,in da uku,yadda kasar ta kwato yankin Sina daga isra,ila.

Masu gudanar da zanga zangar neman gani an hukumta tsohon shugaban
Masu gudanar da zanga zangar neman gani an hukumta tsohon shugabanHoto: dapd

A can dandalin Tahreer kuwa,yadda masu zaman dirshan ke ci gaba da nuna tirjiya,suna kwana a filin Allah duk da tsananin sanyin da ake,a kokarinsu na cimma tabbatar da manufofin juyin juya hali,cewa suke,wannan hukuncin kadan alkalai sun amince dashi,na ɗaya daga cikin abin da suka jima suna fatar ganin ya wakana a kWannan shine mafi karancin hukuncin day a cancanci shugaban kama karya,da kama ya yi ma a yanke wannan hukuncin tun watanni shidan da suka gabata"

Mawallafi:Mahmud Yaya Azare
Edita: Abdourahmane Hassane