Yankin Sinai na Masar na cikin fada
July 3, 2015Dakarun sojin na Masar dai sun ba da sanarwa ci-gaba da kai farmaki ta sama da kasa kan tsagerun mayakan na IS wadanda suka ja daga a garin Sheikh Zuwaid da ke yankin Sinai a arewacin Masar, garin da a jiya da daddare mayakan na IS suka ce sun gama shimfida ikonsu a cikinsa.
Kakakin sojan na Masar dai ya zargi mayakan yankin Gaza da hada baki wajen kai wadannan hare hare:
"A daidai lokacin da ake kawo mana wannan hari, sai mayaka daga yankin Gaza sukai ta harbo mana rokoki,l amarin daya tilastawa dakarunmu na sama maida martani, yadda ya zuwa yanzu aka hallaka 'yan ta,adda 130, kana sojojinmu 17 suka shahada. Wadannan hare-hare manuniya ce ga irin mungun tanadin da makiyanmu ke kitsawa al,ummar Masar, muna shaidawa yan kasa cewa,sai munga bayan wadannan yan ta,adda,ba tare da yin la,akari da asarar rayukan da zamu yi ba."
Tun safiyar Laraba ne dai mayakan na IS suka kaddamar da kazamin harin a yankin na Sinai kan dakrun sojoji da ‘yan Sanda,ta yin amfani da gurneti wajen tarwatsa ofisoshin 'yan sandan yankin, da shingayan bincike ababban hawa 15, da kuma harba rokoki kan barikoki da wuraren hutawar sojoji.
Tun bayan kifar da Mursi, shekaru biyun da suka gabata ne dai, ayyukan tarzoma sukai ta wakana a yankin na Sinai, yankin da yafi ko ina a kasar koma baya, kuma mazauna yankin suka jima suna korafin ana dannesu.
Shugaban kasar ta Masar dai, Abdulfattah al-Sisi, wanda shi ma ya zargi kungiyar 'yan uwa musulmi da kungiyar Hamas da kitsa hare haren na Sinai, ya dauki matakan kawo karshensu ta hanyar rugurguza hanyoyin karkashin kasa da ke kan iyakar yankin da zirin Gaza da kuma tayar da mutane sama da dubu 20 daga gidajensu daga yankin,ba tare da an biyasu diyyar da suka cancanta ba, gami da bawa sojoji umarnin daukar fansa kan wadanda ya kira makiya kasa;
Masharhanta dai na nuna tababa da samun nasara kan yan ta,addar ta hanyar yin watsi da matakan bin doka da sauwwa jami,an tsaro hannu,gami da bin tsagwaron matakan soji.