1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zanga zanga a ƙasar Yemen

February 3, 2011

An yi taho mu gama tsakanin magoya baya da kuma masu adawa da gwamnatin Yemen a birnin Sana'a

https://p.dw.com/p/10AFw
Jerin gwanon nuna adawa da gwamnatin YemenHoto: dapd

Fiye da mutane dubu 20 ne suka yi jerin gwani akan titunan Sana'a babban birnin ƙasar Yemen, domin neman shugaban ƙasar Ali Abdallah Saleh ya sauka daga mulki. Ɗaruruwan masu zanga zangar nuna goyon bayan gwamnati ne dai suka mamaye babban dandalin da ke tsakiyar babban birnin ƙasar da safiyar wannan Alhamis, inda suka tilastawa masu jerin gwanon adawa da gwamnatin sauya akalar zanga zangar da suka yiwa taken "Ranar Nuna Mummunan Fushi" zuwa harabar makarantar jami'ar da ke birnin.

A ƙoƙarin da ya yi na hana gangamin yau Alhamis, jiya Laraba ce shugaba Saleh ya sanar da cewar ba zai nemi wani wa'adin shugabanci ba - idan har wa'adin sa na yanzu ya ƙare a shekara ta 2013. A baya dai shugaba Saleh ya kammala shirin samar da sauyi ga tsarin mulkin ƙasar ta Yemen domin bashi damar ci gaba da mulki har iya tsawon rayuwar sa, amma ya yi watsi da wannan ƙudurin, bisa la'akari da rigingimun da suka ɓarke a ƙasashen Masar da kuma Tunisiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu