1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ta gawurta a Aljeriya

Suleiman Babayo
December 24, 2019

Masu zanga-zanga sun ci gaba da mamaye titunan birnin Algiers na kasar Aljeriya duk da zaman makokin babban hafsan sojojin kasar Ahmed Gaid Salah wanda ya gamu da ajalinsa yana da shekaru 79 sakamakon bugun zuciya.

https://p.dw.com/p/3VIp9
Algerien: Erneute Proteste in Algier
Hoto: Getty Images/AFP

A wannan Talata dubban masu zanga-zanga sun mamaye titunan birnin Algiers fadar gwamnatin Aljeriya, inda suka nuna tirjiya na zaman makokin babban hafsan sojojin kasar Ahmed Gaid Salah wanda ya gamu da ajalinsa jiya Litinin yana da shekaru 79 sakamakon bugun zuciya. Sabon Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya bayyana zaman makokin na kwanaki uku a fadin kasar baki daya.

Masu zanga-zangar suna ci gaba da neman sauyi, kuma su ne suka matsa lamba ga tsohon Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya ajiye aiki inda shi babban hafsan sojojin Marigayi Ahmed Gaid Salah kana yana da karfin fada aji kan hanyoyin tafiyar da kasar lokacin da yake raye.

Tun watan Febrairu ake artabu da masu zanga-zanga galibi matasa 'yan makaranta, kuma zanga-zanga mafi girma da aka gani a kasar da ke yankin arewacin Afirka tun lokacin da ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na faransa a shekarar 1962.