Ci gaba da musayar fursinonin yaki a Ukraine
December 27, 2014Daga nasu bangaren hukumomin na Kiev su ma sun sallami 'yan awaren gabashin kasar akalla 222, kuma hakan ya biyo bayan cimma wata yarjejeniya a birnin Minsk na Belarus a cikin wannan mako. A wannan Asabar din ce dai aka ci gaba da musayar fursinonin tsakanin 'yan awaren gabashin Ukraine da kuma hukumomin kasar, inda nan gaba za a sako wasu sojojinta guda hudu daga Jamhuriyar Lougansk, daya daga cikin yankunan kasar da ya nemi cin gashin kansa. Sai dai ba a bada lokacin yin wannan musaya ba, da ma wurin yin ta.
A ranar Jumma'a ma dai bangarorin biyu sun yi musayar daruruwan fursinoni. Sai dai daya daga cikin sojojin da aka saki na Ukraine ya ki komawa bangaren su, inda ya ce shi dan asalin yankin da ke goyon bayan Rasha ne, kuma baya goyon bayan yadda Ukraine ke daukan matakin soja a gabashin kasar.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal