1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da kame-kamen yan adawa a Burma

October 4, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9O

Jami´an tsaro a ƙasar Burma ko Myanmar, sun ci gaba da kame kamen kai mai uwa da wabi, a sakamakon zanga-zangar gama gari, da yan adawa su ka shirya a ƙasar.

Wani ɗan ƙasar da ya shaidi yadda al´amura ke gudana, ya ce an kama mutane masu yawa, daga daren jiya, zuwa sahiyar yau alhamis, mussaman daga ɓangaren supayen da su ka jagoranci wannan zanga-zanga.

A ɗaya hannun, jami´an tsaron sun fara sako wasu daga cikin mutanen da su ka kama, makon da ya gabata, bayan sun yi masu tambayoyi.

Sakatare jannar na Majlisar Ɗinkin Dunia , ya tabbatar da cewar a gobe juma´a, komitin sulhu zai tantana, a game da rikicin na Burma, bayan wakilin mussamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya gabatar da rahoton rangadin da ya kai, a wannan ƙasa inda ya gana da shugabanin mulkin soja da kuma jagorar yan adawa Au San Suu Kyi.