China za ta kashe wa Afirka Dala dubu 60
December 4, 2015Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa kasarsa za ta kashe kudi Dala miliyan dubu sittin a Afrika kan ayyukan raya kasa da rage basuka da bunkasa ayyukan gona karkashin wani shiri da za a kwashe shekaru uku ana yinsa, wani abu da zai kara karfin fada ajin China a kasashen Afirka.
Shugaba Jinping ya bayyana haka ne a ranar Juma'an nan a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu inda ya ce za su ba wa ayyukan gona muhimmanci cikin wadannan ayyuka.
"Kasar China za ta yi musayar bayanai da kasashen Afirka kan batun da ya shafi ci gaban ayyukan gona, mu kai musu kayayyaki na ayyukan gona na zamani, zamu karfafawa 'yan China gwiwa kan batun zuba jari a ayyukan gona da kiwo a kasashen ta yadda manoma za su sami bunkasar tattalin arziki".
A cewar shugaba Xi Jinping kasar ta China ba zata yi katsalandan ba kan harkokin da suka shafi cikin gida na kasashen na Afirka, wani abu da ya sanya shugabannin na Afirka suka shiga tafi da shewa a wajen taron, musamman shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da kasarsa ke shan sukar kasashen Yamma kan harkokin da suka shafi take hakkin bil'Adama. A gobe Asabar ne dai za a kammala wannan taro na koli tsakanin kasashen na Afirka da China a Afirka ta Kudu.