China: Xi ya zama shugaban sai madi ka ture
March 17, 2018Talla
Zaben dai na zama tamkar cikon doka ne kadai, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta soke takaita wa'adin mulkin shugaban kasar. Hakan na nufin shugaba Xi mutumin da ake yi wa kallon mafi karfi a China, tun bayan Mao Zedong da ya samar da wannan kasa ta kwamunisanci, zai yi shugabancin dindindin mara karshen wa'adi.
Kazalika majalisar da kuri' u 2,969, ta kuma zabi Wang Qishan mai shekaru 69, na hannun daman shugaban kuma mutumin da ya yi suna wajen yaki da cin hanci, a matsayin mataimakin shugaban kasa.