China ta yi martanin haraji kan Amirka
March 23, 2018Talla
A wani mataki na ramuwar gayya kan sabbin takunkumi da kasar Amirka ta sake sanyawa kasar, China ta sanar da zabga haraji kan jerin wasu kayan da ake shigo da su daga Amirka. Sabon takun saka tsakanin kasashen biyu ya biyo bayan dora kudin haraji da ya kai dala biliyan 50 da shugaba Trump ya sa kan wasu kayayyakin China.
Shugaban Amirka ya ce wannnan mataki zai taimaka a seta al'amuran kasuwancin kasarsa, bayan da aka gano China na satar fasaha.
Ma'aikatar kasuwanci da cinikayya ta kasar China, ta bukaci Washington da su sasanta barakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu, amma abin ya ci tura, abinda kuma ake ganin zai kara tsamin danganta tsakanin kasashen biyu.