1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin China ya ja da baya

Abdourahamane Hassane
May 16, 2022

Kasar China ta samu koma bayan tattalin arziki a sakamakon tsauraran matakan da ta dauka na takaita walwalar jama'a saboda annobar corona.

https://p.dw.com/p/4BN4c
China | Coronavirus Lockdown in Shanghai
Hoto: Andy Wong/AP Photo/picture alliance

Karfin tattalin arzkin kasar ta biyu mafi girma a duniya ya ragu fiye da yadda ake tsamani saboda dokar kule da gwamnatin ta kakaba a kasar. Ofisfin kididiga na birnin Bejin a wani rahoton da ya bayyana ya ce haɓakar masana'antu ta faɗi  a cikin watan Afrilu da kashi biyu da digo tara cikin dari,  idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kana rashin aikin yi, ya karu da kishi shida cikin dari.