1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli kan batutuwan da ke addabar Japan da Koriya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 24, 2019

Mahukuntan China da Japan da Koriyya ta Kudu na halartar wani taron koli da zummar tattaunawa batutuwan da dama ciki har da tsamin dangantaka tsakanin Japan da Koriya ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3VI11
China Ostasien-Gipfel
Hoto: picture-alliance/AP/Wang Zhao

A yayin taron kolin da zai shafe tsawon kwanaki biyu ana sa ran Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu  zai gana da firaministan Japan Shinzo Abe, ganawar da suka shafe tsawon watanni 15 ba tare da yin irinta ba bayan wata 'yar tsama tsakanin kasashen biyu. Masana na cewa hukumomin Pekin na bukatar sulhunta bangarorin kasashen da ke cikin wani yanayi na takon-saka inda suke cewa yana da muhimmanci bangarorin kasashen da su cimma wata matsaya guda game da batun makaman nukiliyar Koriya ta Arewa.