China: Sabbin kamun coronavirus sun ragu
February 18, 2020Talla
Hukumomin lafiya a China sun ruwaito sabbin alkaluma 1,886 na sabbin kamun kwayar cutar coronavirus wanda ke zama adadi mafi karanci da aka samu a rana guda a wannan watan. Sabbin alkaluman sun kuma an sami karin mutane 98 da suka rasu a lardin Hubei.
Hukumomin na China sun ce raguwar alkaluman wata alama ce da ke nuna matakan da ake dauka na shawo kan cutar na yin tasiri.
A wannan Talatar hukumomin lafiyar a China sun ce suna aiki don samar da sabin allurai da magungunan cutar da hanyoyin tantace jinin mara lafiya da kuma kare rayuwar likitoci.
A waje guda kuma hukumomin lafiya a Japan sun ce za su fara gwajin amfani da maganin cutar HIV don warkar da marasa lafiya da suka kamu da cutar coronavirus.